Gwamnonin Najeriya sun yi taro a Abuja

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Ana ci gaba da samun rabuwar kai tsakanin gwamnoni

Bangaren gwamnan Pilato, Jonah Jang, na kungiyar gwamnonin Najeriya sun tattauna a game da yadda za a shawo kan yajin aikin da malaman jami'a ke yi a taron da suka yi ranar Lahadi a Abuja.

Kazalika gwamnonin sun tattauna kan gyaran kundin tsarin mulki da satar danyen mai da kuma rikicin da ke tsakaninsu.

A baya dai an samu baraka tsakanin kungiyar gwamnonin kasar abin da ya sa kungiyar ta dare gida biyu.

Gwamna Amaechi ne dai ya lashe zaben da kuri'u 19 yayin da gwamna Jang ya samu kuri'u 16, amma duk da haka bangaren gwamna Jang ya dage cewa shi ne ya lashe zaben.

Wani abu da ya fito fili shi ne rashin halartar bangaren gwamna Rotimi Amaechi na jihar Rivers wajen taron.

Masu sharhi dai na ganin wannan rikici da ke faruwa tsakanin gwamnonin kasar na da nasaba da zaben shekara ta 2015, inda wasu ke goyon bayan shugaba Goodluck Jonathan don ya sake tsayawa takara, wadansu gwamnonin kuwa ke adawa da hakan.

Karin bayani