Sojoji sun kama ƙusa a ƙungiyar Boko Haram

Sojojin Najeriya
Image caption Sojojin Najeriya

Hukumomin sojan Najeriya sun ce sun kama wani da suke zargin cewa jigo ne a kungiyar Boko Haram a birnin Sokoto.

Sojojin sun kuma gano wasu tarin makamai a gidansa.

Kakakin birgade na daya a rundunar sojin Najeriya dake Sokoto, Kaptin Musa Yahaya ya ce kamen ya biyo bayan wani samane na kwanaki biyar tare da hadin gwiwar jami'an tsaro na farin kaya.

Sai dai sojojin ba su ce uffan ba, kan rahotannin kashe wasu mutane hudu da mazauna wata unguwa suka ce sojojin sun yi a karshen mako ba.

Yankin arewacin Najeriya na fuskantar tabarbarewar tsaron saboda ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram.

Karin bayani