An harbe 'yar kwadago a Afrika ta Kudu

Ma'aikatan marikana lokacin da suke tawaye
Image caption Ma'aikatan mahakar Marikana, a wata zanga-zanga

Wata shugabar 'yan kwadago ta rasa ranta, bayan an harbe ta a mahakar ma'adanai ta Marikana dake Afrika ta Kudu.

A ranar litinin ne aka harbe 'yar kwadagon, kuma 'yan sanda sun fara bincike kan lamarin.

Sai dai ba a tantance ko kisan na da nasaba da rikicin dake tsakanin kungiyar masu hakar ma'adanai ta kasa ba da wata kungiyar da aka kirkira a bara.

Zaman dar-dar tsakanin kungiyoyin mahakar ma'adanin Platinum mallakar Lonmin, ya kaiga harbe-harbe a tsawon shekara guda.