Amurka zata yi sauye sauye a tsarin shari'ar ta

Shugaba Obama na Amurka
Image caption Amurka na cikin Kasashen dake da tarin 'yan fursuna.

Gwamnatin Amurka ta bayyana wasu manyan sauye sauye data kawo a tsarin shari'ar manyan laifuka da nufin rage cunkoso a gidajen yarin gwamnati da kuma rage kudaden da ake kashewa.

Babban Lawyan gwamnati Eric Holder ya ce dole ne masu gabatar da kara zasu ajjiye hukunce hukunce daya zama dole mafi kankanta akan wasu shari'oin da suka shafi miyagun kwayoyi.

Mr. Holder ya ce matakan za kuma su taimaka wajen gyara abinda ya kira rashin adalci a tsarin shari'a.

Masu aiko da rahotanni sun ce hukuncen hukuncen da ake yankewa masu ta'ammali da kwayoyi sun fi shafar bakake da kuma Hispaniyawa.

Amurka na daya daga cikin kasashen duniya dake da tarin 'yan fursuna a kurkuku.

Kusan rabinsu na zaman kurkuku ne kuma saboda laifuka da suka shafi miyagun kwayoyi.

Karin bayani