Tsohon minista a Kamaru zai sha dauri

Image caption Urbain Olanguenan Awono

Wata Kotu ta musamman mai shari'ar manyan laifuffuka a Kamaru, ta zantar da hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20 a kan tsohon Ministan kiwon lafiya, Urbain Olanguenan Awono.

Kotun ta same shi da laifin ba da wata kwangila na bogi domin sayen gidajen sauro masu feshin magani.

Haka kuma Mista Awono ya bada wata kwangilar na buga wasu litattafai masu bayani a kan cutar kanjamau a nahiyar Afrika, inda anan ma ya saba ka'ida.

A jimillance sama da miliyan 90 ne na CFA, kotun ta ce sun salwanta a lokacin da shi ministan yake kan mukaminsa.

Sannan kuma hukuncin baya-bayanan ya karu ne a kan wanda wata kotu ta zartar a baya, inda ta yanke mishi hukuncin zaman gidan wakafi na shekaru 15 a kan yin sama da fadi da dukiyar al'umma.

Karin bayani