'Yan sanda sun tarwatsa magoya bayan Morsi

Image caption Magoya bayan Morsi sun yi arangama da masu adawa da shi

'Yan sanda a kasar Masar sun yi amfani da barkonon-tsohuwa don tarwatsa masu goyon bayan hambararren shugaban kasar, Mohamed Morsi, wadanda ke gangami a tsakiyar birnin Alkahira.

Jami'an tsaron sun kai dauki ne bayan magoya bayan Morsi sun yi arangama da abokan adawarsu.

Ganau sun ce bangarorin biyu sun yi ta jefawa juna duwatsu, kuma mata da kananan yara sun tsere daga wajen domin tsira da rayukansu.

Sojojin kasar ne dai suka tumbuke Mr Morsi daga mulkin kasar a watan Yuli, lamarin da ya jawo zanga-zanga.

Sojojin sun nada gwamnatin rikon-kwarya.

Magoya bayan Morsi sun yi fatali da matakin da sojojin suka dauka, kana suka dage cewa dole ne a mayar da shi kan mulki.

Karin bayani