Clinton ya yabi Shugaba Kagame

Shugaba Kagame na Rwanda
Image caption Ana zargin Kagame da goyawa 'yan tawaye baya

Tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton ya yabi Shugaban Rwanda Paul Kagame duk kuwa da zarge zargen da ake masa na cewa yana goyawa kungiyoyin 'yan tawaye baya a jamhuriyar demokradiyar Congo.

A wata hira da BBC, Mr Clinton ya ce zarge zargen, wadanda Rwanda ta musanta, ba a tabbatar da su a gaban kotu ba.

Ya kuma bayyana iyakar dake tsakanin Congo da Rwanda da cewar tana da sarkakiya tunda tana cike da mutanen da suka shirya kisan kiyashi na Tutsi a shekarar 1990.

Amma Mr Clinton ya ce yana baiwa gwamnatin Rwanda kudaden alawus ne saboda irin moriyar tattalin arzikin da ake samu karkashin gwamnatin Shugaba Kagame.

Karin bayani