'Za mu ci gaba da kwace kamfanonin turawa'

Image caption Shugaba Mugabe

Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe ya sha alwashin ci gaba da manufofinsa na tilastawa kamfanonin 'yan kasashen waje koma wa hannun 'yan Zimbabwe.

Wannan manufar itace ya sanya a gaba lokacin yakin neman zaben daya lashe a watan daya wuce.

Mista Mugabe wanda ke kan mulki na tsawon shekaru talatin da uku, ya karyata zargin 'yan adawa cewar an tafka magudi a zabensa.

A wani gangami na zagayowar ranar dakarun tsaron kasar, Mugabe ya ce gwamnatinsa za ta yi duk me yiwuwa don ganin duka kamfanonin kasar sun koma mallakar 'yan Zimbabwe.

Karin bayani