Najeriya ta sa hannu a yarjejeniyar makamai

Image caption Nigeria

Ministan harkokin wajen Najeriya Olugbenga Ashiru ya ce Najeriya ta zamo ta farko a nahiyar Afrika wajen sanya hanu a kan yarjejeniya takaita yaduwar kananan makamai a duniya.

Ya ce Najeriyar ta amince da yarjejeniyar ne, a wani bangare na kokarin da take yi na hana makaman fadawa hannun 'yan ta'adda da masu fashin teku da kuma sauran masu aikata muggan laifuka kamar safarar miyagun kwayoyi da fashi da makami.

Kasar dai na ci gaba da fama da hare-haren da ake zargin kungiyar Boko Haram na kaiwa musamman a yankin arewa maso gabashin kasar, inda ake ganin takaita yaduwar irin wadannan makamai kan iya taimaka wa jami'an tsaron Najeriya wajen shawo kan hare-haren.

Haka zalika masu sharhi a kan al'amura na ganin takaita yaduwar makaman zai taimaka wajen rage karuwar da ake samu a fashin taku da ke dada karuwa a yankin gabar tekun Guinea da kuma rikice-rikicen kabilanci da addini da ma siyasa da ake fama da su a wasu sassan kasar.