Lagos ta daukaka kara a kan Al-mustapha

Image caption Gwamnatin Legas ta ce ba ta gamsu da wankewar da aka yi wa Al-Mustapha ba

Gwamnatin jihar Lagos ta daukaka kara zuwa Kotun Kolin Najeriya game da wanke Manjo Hamza Almustapha da Alhaji lateef Shofolahan da kotun daukaka kara ta yi daga zargin kisan Kudirat Abiola.

Gwamnatin ta Lagos ta ce ta daukaka karar ne saboda ba ta gamsu da hukuncin kotun ba.

An dai wanke, tare da sallamar Manjo Hamza Almustapha, dogarin tsohon shugaban Najeriya, Janar Sani Abacha, bayan ya shafe shekaru 14 a gidan yari.

Al-Mustapha bai mayar da martani game da matakin da gwamnatin jihar Legas din ta dauka ba.

Karin bayani