Bakassi ya koma karkashin ikon Kamaru

Nigeria bakassi
Image caption Yankin Bakassi

Yankin Bakassi ya koma karkashin ikon kasar Kamaru duk da cewa an kwashe shekaru ana mummunan rikici tsakanin Nijeriya da kasar.

Nijeriya ta mika ma kasar ta Kamaru ne yankin na Bakassi shekaru 5 da suka wuce, bayan wani hukunci na Kotun duniya.

Hukuncin ya kawo karshen arangamar da dakarun kasashen biyu suka kwashe shekaru goma suna yi.

A wancan lokaci sai da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe wani lokaci don baiwa 'yan Nijeriya dake zaune a yankin yanke shawarar idan suna so su ci gaba da zama a yankin.

A yanzu dai, dole ne su rubuta takardun izinin neman shiga kasar ta Kamaru ko kuma takardar izinin zama dan kasa idan har suna bukatar ci gaba da zama a yankin.