Ana zubar da jini a Masar

Image caption Mutane da dama sun jikkata

An bayar da rahoton kashe mutane da dama yayin da jami'an tsaron Masar ke yunkurin kawar da sansanonin da magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi ke zaman dirshan a Alkahira.

Sai dai kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, wato Muslim Brotherhood, wacce ke goyon bayan zaman dirshan din, ta bayar da alkaluman wadanda suka rasa rayukansu sama da haka.

An ji karar harbe-harbe lokacin da manyan motoci masu rushe-rushe suka isa wurin; jami'an tsaro kuma sun yi ta harba hayaki mai sa hawaye.

Hukumomi sun ce tuni suka share sansanin zaman dirshan na Dandalin Nahda dake yammacin Alkahira.

Karin bayani