Yunkurin tarwatsa magoya bayan Morsi a Masar

Yunkurin kawar da masu zanga-zanga
Image caption Yunkurin kawar da masu zanga-zanga

Jami'an tsaro a Masar na kokarin kawar da magoya bayan hambararren shugaban kasar Masar Muhammad Morsi da ke zaman dirshan a cibiyoyi biyu na birnin Alkahira.

Rahotanni na cewa mutane da dama sun rasa rayukansu kawo yanzu.

Rahotanin sun kuma ce an yi amfani da harsasai na zahiri a kan masu zanga zangar da barkonon tsohuwa a sansanon biyu.

Ma'aikatar al'amuran cikin gidan kasar ta Masar ta ce a yanzu ta kammala tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Morsi daga dandalin Nahda da ke kusa da jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira.

Jami'an tsaron sun ce suna harba hayaki mai sa hawaye a babbar cibiyar masu zanga-zangar da ke masallacin Rabaa.

Masu zanga-zangar sun shafe fiye da makwanni shida suna zaman dirshan a gaban masallacin da kuma dandalin Nahda duka a birnin Alkahira.

Ma'aikatar al'amuran cikin gidan kasar ta ce za ta kyale masu zanga-zangar su fice ba tare da zubar da jini ba.

Karin bayani