Rashin lafiyar Fidel Castro

Cuba
Image caption Tsohon shugaban kasar Cuba Fidel Castro

Tsohon Shugaban kasar Cuba Fidel Castro ya yi karin haske a kan dalilin da yasa ya sauka daga karagar mulki a shekarar 2006.

A cewarsa , ya yanke shawarar baiwa Kaninsa Raul Castro ragamar Shugabancin, saboda likitoci sun shaida masa yana tare da wani ciwo da ba zai yi tsawon rai ba.

A wasu bayanai da aka buga don bukin cikarsa shekaru tamanin da 7 a duniya, Fidel Castro ya ce, bai yi zaton ciwon cikin da yake fama da shi ba zai sa ya kara wasu shekaru bakwai a raye.

Fidel Castro din ya kuma bayyana cewar Tarayyar Soviet ta gargade shi a shekarun 1980 cewar ba za ta iya ci gaba da baiwa kasar ta shi kariya ba, idan Amurka ta kai ma ta hari.