Israila da Palasdinawa na tattaunawa

Birnin Kudus
Image caption Birnin Kudus

Wakilan Isra'ila da na Palasdinawa sun hallara a birnin Kudus, domin taron keke-da-keke a karon farko cikin shekaru uku.

Masu aiko wa BBC rahotanni sun ce sanarwar da Isra'ilar ta yi na ranar Lahadi, na gina sabbin matsuganai a yankunan Plasdinawan da ta mamaye ne zai kankane tattaunawar.

Can a gabar yamma da kogin Jordan kuwa, Palasdinawa ne ke bukuwan sakin fursunoni 26 da Isra'ila ta yi.

Su ne dai kashi na farko na fursunoni fiye da dari da Isra'ilar za ta sake, a wani bangare na maido da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.