'Sojoji na samun galaba a kan Boko Haram'

Ministan harkokin cikin gidan Najeriya, Abba Patrick Moro
Image caption Ana cigaba da samun hare-hare daga kungiyar Boko Haram duk da dokar ta-baci a jihar Borno da Yobe

Ministan harkokin cikin gidan Najeriya, Abba Moro, ya ce sojoji na samun galaba a kan mayakan kungiyar Boko Haram.

Ya ce, "harin na baya-bayan nan wani karfin hali ne 'yan Boko Haram ke yi, domin nuna cewa har yanzu suna nan da karfinsu."

Ministan yace, sojojin kasar sun kori 'yan gwagwarmayar daga manyan wuraren da suka yi babakere.

A ranar Lahadin da ta wuce ne aka kashe wasu mutane 44 a Masallaci a garin Konduga, harin da aka dora alhakinsa kan Boko Haram.