MSF za ta dakatar da ayyukanta a Somalia

Image caption Shugaban MSF, Unni Karunakara

Kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontieres (MSF) za ta dakatar da dukkan ayyukanta a kasar Somalia bayan shafe shekaru ashirin da biyu tana aiki a cikin kasar da yaki ya daidaita.

Wata sanarwa, ta ce matakin ya biyo bayan munanan hare-hare da ake kaiwa ma'aikatanta.

A cewar kungiyar kungiyoyin masu rike da makamai da shugabannin fararen hula na "goyon baya tare da kawar da kai a kan sace ma'aikatan agaji".

Fiye da ma'aikata 1500 ne ke gudanar da ayyukan kungiyar ta MSF a kasar ta Somalia.

Shugaban MSF Unni Karunakara, ya ce wannan mataki ne mai wuyar gaske da suka dauka.

A shekarar 1991, lokacin da Somalia ta afka a cikin yakin basasa, an kashe ma'aikatan MSF su 16, sannan an kaiwa ma'aikata da dama hari.

Karin bayani