Atiku na yunkurin kafa sabuwar jam'iyya

Nigeria atiku
Image caption Alhaji Atiku Abubakar

Rahotanni sun nuna cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar da wasu na wani yunkuri na kafa wata sabuwar jam'iyyar siyasa mai suna PDM, wato Peoples Democratic Movement.

Kafa jam'iyyar kamar yadda wasu ke cewa za ta ba shi damar yin zabi idan jam'iyyarsa ta PDP ta nemi taka masa birki game da burinsa na siyasa a nan gaba.

Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasar a nasa bangaren ya ce babu hannunsa a wannan yunkuri, amma da wasu aminansa na siyasa a cikin tafiyar.

kakakin tsohon mataimakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya shadaiwa BBC cewa kawo yanzu Atiku cikakken 'dan PDP ne.