'Yan Najeriya a Bakassi na tsaka mai wuya

Image caption Galibin al'ummar Bakassi masunta ne

'Yan Najeriya da ke zaune a tsibirin Bakassi, wanda ya koma mallakin Jamhuriyya Kamaru, suna can cikin tsaka mai wuya.

Hakan ya biyo bayan zabin da hukumomin na Kamaru suka ba su a kan ko dai su cike takardun zama 'yan Kamarun, ko kuma su ci gaba da zama a wurin a matsayinsu na 'yan Najeriya, amma su rika biyan haraji, ko kuma su san na yi.

Hakan nan kuma jama'ar tsibirin na Bakassi da suka yanke shawarar koma wa Najeriya tun wajen shekaru biyar da suka gabata dai, su ma suna kukan an yi watsi da su.

Najeriya ta mika ma kasar ta Kamaru ne yankin na Bakassi shekaru 5 da suka wuce, bayan wani hukunci na Kotun duniya.

Hukuncin ya kawo karshen cece-kuce tsakanin kasashen biyu da aka shafe shekara da shekaru suna yi.

Karin bayani