Tattaunawar zaman lafiya a Gabas ta tsakiya

Ban ki  moon
Image caption Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon

Idan an jima a yau ne sakatare janarar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki moon zai gana da Shugabannin Isra'ila .

Mr Ban na ziyarar yankin ne don nuna goyon baya ga farfado da shirin tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.

A ranar alhamis, Mr Ban, ya ce, yana cikin matukar damuwa da aikin da Isra'ila ke yi na cigaba da gina matsugunan yahudawa a gabashin birnin Kudus da Gabar Yamma ta Kogin Jordan.

Mr Ban ya ce, fadada matsugunan na Yahudawa a yankin yana kara sa Palasdinawa su nuna rashin amincewa da aniyar Isra;ila.