An wayi gari cikin rashin tabbas a Masar

Image caption An yi hasarar rayuka da dama

Birnin Alkahira na Masar ya kasance shuru amma cikin yanayi na zaman dar dar, bayan da aka diranma masu zanga-zanga, lamarin daya janyo mutuwar mutane da dama.

Kasasashen duniya sun yi Allawadai da matakin sojin.

Akalla mutane 421 sun mutu lokacin da jami'an tsaro suka kutsa cikin sansanoni biyun da magoya bayan hambararren shugaban Masar, Muhammad Mursi suka kafa a watan daya gabata.

An kafa dokar ta-baci da kuma ta takaita zirga-zirga a birannen Masar a kokarin yayyafa ruwa ga kurar rikicin data taso.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ce lamarin zai kawo cikas a yinkurin sasantawa.

Shugabar manufofin kasashen waje ta kungiyar tarayyar Turai, Catherine Ashton da Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon sun soki matakin amfani da karfin soji.

Wakiliyar BBC Bethany Bell a birnin Alkahira, ta ce Misirawa sun wayi gari cikin fargaba da rashin sannin tabbas a kan makomarsu.

Karin bayani