An tabbatar da nasarar Keita a hukumance

Image caption Ibrahim Boubakar Keita

Sakamakon zaben shugaban kasa da aka fitar a hukumance a kasar Mali ya tabbatar da nasarar Ibrahim Boubakar Keita da gagarumin rinjaye.

Alkaluma sun nuna cewar Mista Keita ya lashe fiye da kashi saba'in da bakwai cikin dari na kur'iun da aka kada.

A wata mai zuwa ne za a rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasa.

Zaben ya biyo bayan fiye da shekara daya da aka shafe ana cikin wani irin yanayi a kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Sannan kuma dakarun kasar Faransa suka fatattaki 'yan tawaye wadanda suka kwace iko a arewacin Mali.

Tun kafin zaben, Mista Keita ya ce abin da zai bai wa fifiko shi ne hada kan kasa.

Karin bayani