Karuwar ambaliyar ruwa a Najeriya

Image caption Ruwa ya lalata gidaje da dama

Ana ci gaba da fuskantar ambaliya sakamakon ruwan sama da ya haddasa ta'adi mai dimbin yawa a wasu sassan Najeriya.

Ambaliyar ta yi daidai da hasashen masana a kan cewar jihohi da dama a kasar za su fuskanci ambaliyar ruwa musamman a jihohin Bauchi da Gombe.

Wasu daga cikin abubuwaan da kan ta'azzara girman ta'adin dai a cewar masana, sun hada da rashin ingantattun magunan ruwa da toshewar wadanda ake da su, da kuma yadda wasu jama'a suke yin gini a hanyoyin ruwa.

Kawo yanzu dai a bana mutane da dama sun rasa muhallansu sakamakon ambliya.

A shekarar da ta gabata dubban mutane sun rasa gidajensu a Najeriya, sannan kuma wasu sun gamu da ajalinsu bayan ruwa kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliya.

Karin bayani