NEMA ta shawarci sojoji a kan barikinsu

Image caption Janar Ihejirika

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA ta ba da umarnin tayar da wani bangaren barikin sojoji na tamanin da daya da ke tsibirin Victoria a birnin Legas.

Umarnin ya biyo bayan barazanar da torokon da ruwan teku ke yi ga barikin.

Tuni dai wasu gine-gine na barikin da aka gina tun zamanin turawan mulkin mallaka suka fara rugujewa.

Haka kuma ruwan tekun ya soma malala cikin 'yar kasuwar da ke cikin barikin da ake kira 'Mami Market' da kuma wasu wurare da manyan jami'an sojojin ke hutawa a barikin na Legas.

Jami'in NEMA a legas, Ibrahim Fayoleye ya ce "bayan mun je mun ga yadda girman matsalar take, ganin cewa tudannin da aka tanada don tare ruwan tekun sun zaizaiye, wannan kuma shi ya sa ruwan ya fara cinye wani bangare na barikin".

Karin bayani