MDC ta janye karar ta a kan Mugabe

Image caption Shugaba Mugabe da Morgan Tsvangirai

Babbar jam'iyyar adawa ta kasar Zimbabwe ta janye karar da ta shigar na kalubalantar sake zaben Robert Mugabe a watan da ya gabata.

Jam'iyyar MDC ta ce tana shakku a kan ko za a yi ma ta adalci a karar da ta shigar tana zargin tafka maguda a zaben.

A cewar jam'iyyar, watakila jami'ai su boye wasu abubuwan shaida a kan kura-kuran da aka yi lokacin zaben.

Amma MDC din ta shigar da wata karar, don a ba ta damar samun dukkan bayanan sakamakon zaben daga wajen hukumar zabe.

Mista Mugabe wanda ke kan mulki tun a shekarar 1980, ya bayyana wa wadanda suka soki zabensa da su kashe kansu.

Karin bayani