An kai hari kan sansanin gine-gine a Afghanistan

Hari a kasar Afganistan
Image caption Hari a kasar Afganistan

Mahukunta a Afghanistan sun ce wasu masu tada kayar baya sun kai hari a sansanin ma aikin gine-gine a gabashin Lardin Herat, suka hallaka mutane 9.

Ma'aikatan na gudanar da aikin ginin hanya ne wanda kasar Jamus ta daukin nauyi.

Jami'an kasar ta Afghanistan sun ce ma'iakatan gine-ginen na tsakiyar barci ne lokacin da aka kai musu wannan hari.

Suna dai gudanar da aikin ginin hanya mai nisan kilomita hamsin ne wanda gwamnatin Jamus ke daukar nauyi.

Babu da wata kungiya da ta fito ta yi ikirarin kai wannan hari.

Wani jami'i ya ce ana zargin 'yan kungiyar Taliban ne suka kaddamar da wannan hari, da aka yi amfani da makaman rokoki da bindigogi masu sarrafa kansu.

An kuma hallaka iyalai biyar 'yan gida guda, da suka hada da mace da yara, a wani harin bom da aka kai a bakin hanya a arewacin Lardin Helmand.

A watannin baya bayan nan dai yawan kai hare-hare sun kara ta'azzara a kasar ta Afghanistan.

Hakan na zuwa yayin da dakarun kasar ke kan karbar ragamar jagorancin al'amuran tsaro daga takwarorinsu na kasashen waje.