An rantsar da Michel Djotodia a matsayin shugaban kasa

Michel Djotodia
Image caption Michel Djotodia

Jagoran 'yan tawayen da suka kwace mulki a Jumhuriyar Tsakiyar Afrika can baya a bana,

Michel Djotodia, an rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.

Mr Djotodia ya ce yana da aniyar gudanar da zabe a kasar a karshen badi.

Tunda ya kwaci mulkin a watan Maris, a matsayin jagoran kungiyar 'yan tawaye ta Seleka, kasar ta kara aukawa cikin talauci da rashin bin doka.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa sulusin mutanen kasar suna bukatar agajin jin kai.

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa rugujewar bin doka a Jumuhuriyar ta Tsakiyar Afrika, zai yi gagarumar barazana ga zaman lafiyar yankin.