'Yan Kungiyar Ikhwan 38 sun mutu a kurkukun Masar

Magoya bayan Muhammad Mursi
Image caption Magoya bayan Muhammad Mursi

'Yan kungiyar 'Yan'uwa Musulmin su talatin da takwas sun rasa rayukansu, aka ce a lokacin da suke kokarin tserewa daga gidan yari a waje da Alkahira, babban birnin kasar.

A cikin wata sanarwa, Ma'aikatar Cikin Gida ta ce 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa don kwato sauran wani jami'in da fursunonin suka yi garkuwa da shi.

Ma'aikatar ta haramta kwamitocin jama'a, wadanda mutane suka kakkafa don kare unguwanninsu, saboda an yi amfani da su don yin aikin daba.

Kafin sannan kuma, a wani taro na majalisar ministoci ta wucin gadi, an yi nazari a kan gidan talabijin na Aljazeera.

Karin bayani