'Yan Syria na kara shiga cikin Iraqi'

Sansanin 'Yan gudun hijrar Syria
Image caption 'Yan Syria na shiga Kasashen Labanon da Jordan da Turkiyya

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya tace an samu karuwar 'yan gudun hijirar dake shiga cikin Iraqi daga Syria.

Jami'ai sun ce 'yan gudun hijira dubu goma ne suka haura cikin Iraqi a ranar asabar, bayan guda dubu bakwan da suka isa kasar a ranar Alhamis.

Mafiyawancin 'yan gudun hijirar ga alamu iyalan kurdawa ne da suka tsere daga wani yanki da ake fama da tashin hankali da kungiyoyin da ake alakantawa da Al-Qaida.

Jami'an majalisar dinkin duniya sunce sun ga motocin safa- safa suna sauke mutane.

Daga nan sai mutanen suka tsallaka cikin Iraqi ta kan wata gada da aka gina kwanan nan.

Wani mai magana da yawun hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya ya ce 'yan Syria fiye da miliyan daya da dubu dari tara ne suka tserewa yakin, mafiyawancinsu kuma sun shiga ne cikin kasashen Labanon da Turkiyya da kuma Jordan.

Karin bayani