An kori Tareq Al-Suwaidan daga aikinsa

Sarki Abdallah na saudiyya
Image caption Tareq Al-Suwaidan na sukar gwamnatin Masar

An kori fitacccen mai wa’azin nan na Kuwait Tareq Al-Suwaidan daga aikinsa na daraktan Tashar Talabijin ta addini a Saudi Arabia saboda alakar sa da Kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi.

Mutumin da yake mallakar tashar Yarima Alwaleed bin Talal ya ce mambobin ‘yan uwa musulmi basu da gurbi a harkokin kasuwancinsa.

Mai wa’azin dai ya kasance yana sukar gwamnatin rikon kwaryar Kasar dake samun goyan bayan sojojin Masar saboda hanbarar da Shugaba Morsi.

A ranar Juma’a Sarki Abdallah ya yi kira akan larabawa dasu ki abinda ya bayyana shi da cewa yunkuri na dagula al’amura a Masar

Karin bayani