Za a sake bude ofishin jakadancin Birtaniya a Yemen

Jami'an tsaron Yemen a gaban ofishin jakadancin Birtaniya
Image caption Jami'an tsaron Yemen a gaban ofishin jakadancin Birtaniya

A yau ne za'a sake bude ofishin jakadancin Birtaniya dake kasar Yemen, bayan rufe shi na tsawon kwanaki goma sha daya saboda batun tsaro.

Birtaniya na daga cikin kasashen da suka rufe ofisoshin jakadancinsu, tare da janje ma'aikatansu, bayan da Amurka ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar kungiyar al-Qaeda zata kai musu hari.

Jami'an tsaron Amurkar dai sun ce sun samu wasu bayanai ne tsakanin shugaban kungiyar Ayman al-Zawahiri, da kuma jagoran kungiyar na kasar Yemen-Nasser al-Wuhayshi.