Ambaliyar ruwa ta kashe 106 a china

Wasu mutane a cikin kwale-kwale a kasar Sin
Image caption An kwashe mutane kimanin dubu 840 daga guraren da ambaliyar ta shafa

Akalla mutane 106 ne suka mutu, wasu 111 kuma suka jikkata sakamakon ruwa kamar da bakin kwarya da ya janyo ambaliyar ruwa a China.

Ana tsammanin ambaliyar ta shafi mutane kimanin miliyan takwas a arewa-maso-gabashi da kudancin kasar.

Ambaliyar ruwan ta janyo katsewar zirga-zirgar jiragen kasa da na motoci da kuma katsewar wutar lantaki a Fushun.

Rahotanni na cewa kimanin sojoji dubu uku ne ke taimaka wa wajen kai dauki.