An tsare mutane fiye da 2000 a Masar

Image caption Sojoji sun damke wata mata

Adadin mutanen da ma'aikatar harkokin cikin gidan Masar ta ke tsare dasu a cikin 'yan makwannin nan.

-Mutane 263 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka tsare a ranar 16 ga watan Agusta a dandalin Ramses wasu sunsu 'yan kasar Syria da Pakistan ne.

-Mutane 275 aka tsare a ranar 17 ga watan Agusta saboda saba dokar hana fita da aka kafa.

-Magoya bayan 'Yan Uwa Musulmi su 1,004 aka tsare a daukacin kasar Masar a ranar 16 ga watan Agusta, wato ranar da aka kawar da magoya bayan a Rabaa da kuma Nahda.

-An tsare mutane 50 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a yankin Tanta a ranar 17 ga watan Agusta.

-Mutane 385 aka tsare a Masallacin Fatah a ranar 17 ga watan Agusta ciki hadda 'yan kasar Ireland da Turkiya da kuma Syria.

-An tsare mutane 36 a Iskandiriya a ranar 18 ga watan Agusta saboda saba dokar hana fita.

-Mutane 157 na kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ne aka tsare a ranar 19 ga watan Agusta.

-Shugabannin kungiyar 'Yan Uwa Musulmi su 6 ne aka tsare a Matrouh a ranar 19 ga watan Agusta.

Akwai kuma rahotannin dake nuna cewar an tsare magoya bayan hambararren Shugaban na Masar, Muhammed Morsi da dama a larduna daban-daban, amma kawo yanzu ba a san yawansu ba.

Karin bayani