An kama shugaban 'Yan Uwa Musulmi

Shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi Mohammed Badie
Image caption Kamun da aka yi wa Mohammed Badie koma-baya ne ga kungiyar 'yan uwa Musulmi

Kafar watsa labarai ta kasar Masar ta bayyana kama shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, Mohammad Badie, a Alkahira babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce ana tsare da shi a wani gida da ke gabashin gundumar birnin Nasr.

Birnin na Nasr na daga cikin manyan wuraren da magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi suka yi zaman-dirshan .

Jami'an tsaro sun tarwatsa su a makon jiya.

Wakilin BBC ya ce kama Mohammad Badie wata babbar mahangurba ce ga kungiyar 'yan uwa Musulmi, a wannan yanayi da mahukuntan kasar ta Masar ke bin diddigin shugabanninsu a fadin kasar.