Zaman makokin kwanaki uku a Masar

  • 20 Agusta 2013
Zaman makoki a kasar Masar
Image caption Zaman makoki a kasar Masar

Gwamnatin rikon kwaryar kasar Masar ta sanar da fara zaman makokin kwanaki uku na jami'an 'yansanda 25 da aka kashe ranar Litinin.

'Yansandan sun mutu ne a wani kwanton bauna da wasu da ake zargi masu tsattauran kishin addinin Islama ne suka kai musu a yankin Sinai.

Babban Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, ya yi Allah Wadai da wadannan kashe-kashe.

A lokaci guda kuma, Mr Ban ya ce ya damu matuka game da mutuwar fursunoni 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi kimanin 37 a ranar Lahadi.

A cewar mahukuntan kasar ta Masar sun mutu ne a sakamakon shakar hayaki mai sa hawayen da suka yi lokacin da suke yunkurin tserewa.

Mr Ban dai ya yi kira da a gudanar da bincike game da lamarin.

Majalisar Dinkin Duniya

Babban Sakataren Majalisar Dinikin Duniya Ban Ki-Moon ya kuma ce Majalisar dinkin Duniya za ta taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen rikicin siyasar kasar ta Masar.

Yayin da yake magana a taron manema labarai a Helkwatar Majalisar Dinkin Duniyar dake birnin New York, Mr Ban ya ce za a tura wakili zuwa birnin Alkahira wanda zai tattauna da duka bangarorin.

Ya ce Majalisar Dinkin Duniya a shirye take da ta marawa Misirawa baya, da tunkarar shawo kan matasalar rikicin da ke faruwa.

Ya umarci Mataimakin Babban Sakatare Janar mai lura da harkokin siyasa, Mr Jeff Feltman da ya gudanar da doguwar tattaunawa a birnin Alkahira daga gobe.

Za kuma a maida hankali wajen yadda Majalisar Dinkin Duniya za ta taimaka wajen maido da zaman lafiya a kasar.'

A baya dai masu shigar da kara a Masar sun gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan hambararren shugaban kasar mai ra'ayin addinin musulunci Muhammad Morsi, in da su ka ce za a tuhume shi da rura wutar rikicin.