Habasha ta yi yarjejeniya da kamfanin ZTE

Kasar Ethiopia
Image caption Kasar Ethiopia

Kasar Habasha ta sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci, na kimanin dala miliyan 800 da wani kamfanin sadarwa na kasar Sin mai suna ZTE.

Yarjejeniyar ta kunshi fadada hanyoyin sadarwar wayoyin salula da suka hada da inganta hanyoyi Intanet na tafi da gidanka wanda yayi matukar karanci a kasar.

Kamfanin sadarwa na Habasha wato Ethio Telecom, ya ce yarjejeniyar na daga cikin manufofin gwamnati na bunkasa tattalin arzikin kasar nan da shekarar 2025.

A watan da ya gabata ne kasar ta sanya hannu kan wata yarjejeniya makamanciyar wannan, da kamfanin Huawei na kasar Sin.