Jakadun Tarayyar Turai za su gana

Kasar Masar
Image caption Kasar Masar

A yau ne Jakadun kasashen Tarayyar Turai za su yi wani taron gaggawa, don tattauna rikicin da ake fama da shi a kasar Masar.

Ana sa ran jakadun za su tattauna matakan da kungiyar za ta dauka game da rikicin, wanda ya hada da rage yawan kudaden tallafin da kungiyar ta yi alkawarin baiwa kasar ta Masar.

A wata sanarwa ta hadin guiwa, shugaban hukumar tarayyar da shugaban Majalisar koli ta Tarayyar Turan, sun bayyana cewa babu hujjar da za'a iya bayarwa ta kisan jama'a a 'yan kwanakin nan.

To sai dai Kasar Saudiya ta gargadi kasashen Turai, da su daina matsin lamba ga gwamnatin rikon kwarya ta kasar Masar, da ke kokarin dakile zanga-zangar magoya bayan 'yan kungiyar 'Yan'uwa Musulmi.