Bikin tunawa da ma'aikatan agaji

Image caption Ma'aikatan agaji na fuskantar kalubale

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce a bana masu aikin agaji 76 ne suka rasa rayukansu a duk duniya a lokutan da suke gudanar da ayyukan jin-kai.

A Najeriya a cewar hukumar kusan ma'aikatan agaji goma sha biyar ne suka mutu a wajen aikinsu.

Hukumar dai ta bayyana hakan ne yayin bikin ranar tunawa da kuma karrama ma'aikatan agajin da suka rasa rayukansu a lokacin da suke gudanar da ayyukansu da ake gudanarwa shekara-shekara.

Majalisar dinkin duniya ce ta kebe wannan ranar don bikin zagoyar bam din da aka dasa a shalkwatar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Iraqi a shekara ta 2003, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 22.

Karin bayani