Jirgin kasa ya kashe mutane 27 a India

Image caption Wasu daga wadanda suka tsira da ransu

Jami'an tashar jiragen kasa a India sun ce akalla mutane ashirin da bakwai ne suka rasa rayukansu a lokacin da jirgin kasa ya buge su a gabashin birnin Bihar.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen na tsallaka layin dogo a tashar jirgin da ke kusa da wurin da suke bauta a lokacin da jirgin ya buge su.

Jami'an sun ce gawarwakin na cikin yanayi maras kyau, da ya hana tantance yawan mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Bayan aukuwar lamarin ne, wasu mutane da suka cinna wuta tare wawashe kayayyakin cikin tashar da ke Dhamara Ghat mai nisan kilomita dari da tamanin da birnin Patna.

Daruruwan mutane na rasa rayukansu a India a kowacce shekara a wajen bautar.

Karin bayani