'An bukaci a janye takunkumi a kan Zimbabwe'

Image caption Shugaba Robert Mugabe

Shugabannin kungiyar kasashen Kudancin Afrika-SADC sun yi kira ga kasashen duniya dasu janye takunkumin da aka sanya wa kasar Zimbabwe.

Sabuwar shugabar kungiyar SADC Joyce Banda, ta ce irin wahalar da 'yan kasar Zimbabwe suka shiga sakamakon takunkumin ta isa haka.

Misis Banda wacce ita Shugabar Malawi ta ce "ya kamata kasashen duniya su sake nazari kan matsayin da suka dauka na sanya takunkumi ganin irin ci gaban da aka samu a Zimbabwe".

Shugabannin sun kuma bayyana gamsuwar su game da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar ta Zimbabwe inda suka taya Mista Mugabe da jam'iyyarsa ta Zanu-PF murnar nasarar lashe zaben.

Sai dai jagoran 'yan adawa Morgan Tsvangarai tare da wasu masu sa'ido kan yadda aka gudanar da zaben, sun yi korafin cewa an tafka kura-kurai.

Karin bayani