An tuhumi El Baradei da cin amanar kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa a gwamnatin riƙon ƙwarya ta Masar, Mohamed El-Baradei zai fuskanci tuhumar cin amanar kasa saboda murabus din da ya yi cikin makon da ya gabata.

ElBaradei ya yi murabus ne domin nuna taikaici dangane da kisan magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi da da dakarun Masar suka yi.

Mai gabatar da ƙara ya ɗau matakin tuhumar El-Baradei ne bayan wani dan kasa a ƙashin kansa ya koka da cewa, murabus ɗin da yayi tamkar ya nuna gwamnati tayi amfani da ƙarfi da ya wuce ƙima akan masu zanga-zanga.

Idan har aka same shi da laifi, El-Baradei zai fuskanci tarar dalar Amurka dubu goma sha biyar.