ICC ta umarci Ruto ya halarci zamanta

Mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto
Image caption Kotun na tuhumar karin wasu mutane hudu a Kenya, ciki har da shugaban kasar Uhuru Kenyatta

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya, ta yanke hukuncin cewa, dole a halin yanzu mataimakin shugaban kasar Kenya, ya rinka halartar duk zaman kotun kan tuhumar da ake masa.

Ana dai tuhumar Mr. Willaim Ruto da hannu a cikin barkewar babban rikicin kasar da ya biyo bayan zaben da aka yi a shekarar 2007.

Matakin kotun ya biyo bayan bukatar da mai shigar da karar ta yi na cewa, Mr. Ruto ya rinka halartar zaman kotun da ake yi a Hague, har sai an yanke hukunci a kan daukaka karar.

Za a fara sauraron karar ne daga ranar goma ga watan Satumba, kuma ba a bayyana ranar da za a yanke hukunci ba.