Miranda zai yi karar mahukuntan Birtaniya

Mr David Miranda da abokin aikinsa Glenn Greenwald
Image caption Mr David Miranda da abokin aikinsa Glenn Greenwald

Dan asalin kasar Brazil din nan da aka tsare a filin jiragen sama na Heathrow dake London, Mr David Miranda ya ce zai yi sammacin mahukuntan Birtaniya.

An dai tsare Mr Miranda ne har na tsawon sa'o'i tara, karkashin wasu dokokin yaki da ta'addanci na Birtaniya.

Mr Miranda ya ce ya bai wa masu tuhumarsa lambobin sirrin adireshinsa na email da na dandalin sada zumunta, saboda maimaita barazanar da ake yi masa na fuskantar zaman gidan yari idan bai aikata hakan ba.

Ya kuma ce zai shigar da kara kan mahukuntan Birtaniya, don su dawo masa da duka na'urorin lataroninsa da aka kwace.

Mr Miranda ya shaidawa BBC cewa bayyana lambobin sirrin nasa da ya yi, ya sa yana jin tamkar an tube shi tsirara ne a bainar jama'a.

Bayanai dai sun ce Mista Miranda, na matsayin dan aike ne na Glenn Greenwald, dan jaridar Guardian, da ya yi hira da tsohon jami'in hukumar leken asirin Amurka Edward Snowden wanda ke neman mafaka.