Babu ranar janye yajin aiki —ASUU

Image caption Ministar Ilimi, Rukayyatu Rufa'i

Kungiyar malaman Jami'o'i ta kasa a Najeriya watau ASUU ta yi kashedin cewa babu wata rana ta janye yajin aikin da yanzu haka take yi muddin gwamnatin kasar ta gaza wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla da ita a shekara ta 2009.

Kungiyar ta ASUU ta furta haka ne bayan an gaza cimma matsaya a tattaunawar baya-bayan nan da suka yi da mukarraban gwamnati dangane da yunkurin da gwamnatin ke yi na kawo karshen yajin aikin.

Shugaban kungiyar ta ASUU, Dr Nasiru Isa Fagge ya ce sun lashi takobin ci gaba da yajin aikin ne saboda kalaman da Ministar kudin ta yi game da yarjejeniyar wadanda ya ce sun lura an ma raina musu wayau.

Kusan watanni biyu kenan da aka rufe jami'o'in Najeriya sakamakon yajin aikin malamai.

Rahotanni sun cewar, Shugaba Goodluck Jonathan na shirin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan batun don a warware takaddamar.