Kotu a Masar ta ba da umurnin sakin Husni Mubarak

Image caption Hosni Mubarak

Wata Kotu a Masar ta ba da belin tsohon Shugaban kasar Hosni Mubarak, wanda ake zarginsa da cin hanci.

Babu tabbas ko a yaushe zai bar gidan yari, saboda masu shigar da kara za su iya kalubalantar shari'ar.

Lauyoyinsa sun ce za a iya sallamarsa a ranar Alhamis.

Mai shekaru 85 a duniya, Mubarak zai kara fuskantar shari'a bisa zargin hannu a kisan masu zanga-zanga, lokacin boren da ya kai ga hambarar da gwamnatinsa a shekara ta 2011.

A bara aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai, amma kuma sai ya daukaka kara, abin da ya bada damar sake shari'ar.

Masu aiko da rahotanni sun ce wannan matakin babban koma baya ne, ga wadanda suka yi juyin-juya halin kawar dashi a kan mulki.

Matakin na zuwa ne makwanni kadan bayan da aka hambarrar da zababben shugaban Masar, Mohammed Morsi.

Karin bayani