Shirin samar da intanet ga 'yan Afrika

Mai shafin sada zumunta na Facebook, Mark Zuckerberg
Image caption Kamfanonin sun ce kimanin biliyan 2.7 na mutanen duniya ne ke samun hanyar sadarwa ta intanet

Wanda ya kirkiro shafin sada zumunta na Facebook, Mark Zuckerberg ya kaddamar da wani shiri na samar da hanyar sadarwa ta intanet ga 'yan Afrika biyar.

Shirin na hadin gwiwa ne tsakanin shafin da kamfanin lataroni na Ericsson da Media Tek da Nokia da Qualcomm da Samsung da sauransu.

Shirin na da aniyar saukaka farashin samun bayanai ta wayar salula.

Kamfanonin dai sun ce suna son taimakawa kasashe masu tasowa, su shiga sawun al'umomin dake mu'amala da intanet.

Masana

Mr. Zuckerberg ya ce manufar ita ce samar da intanet ga wadanda a yanzu ba su da halin mallakarta.

Wata sanarwar da kamfanonin suka fitar, ta ce mutane biliyan biyu da miliyan dari bakwai, wato kashi daya bisa uku na mutanen duniya ne ke samun intanet.

Samun karbuwar intanet na sauri da kasa da kashi tara cikin dari a shekara, abin da suke ganin baya sauri.

Abu mafi mahimmanci a shirin dai shi ne yin bincike, domin gano hanyoyin da za su yi amfani da bayanai kadan don sanya wa a shafukan intanet da a manhajoji.

Dr. Micheal Jennings, shugaban sashen nazarin nahiyar Afrika a jami'ar London ta Soas, ya ce shirn abin yin maraba ne, amma akwai abubuwa masu muhimmanci kamar samar da wutar lantarki mai dorewa.