Manning zai sha daurin shekaru 35

Image caption Bradley Manning

An yakewa sojan Amurka wanda ya mika bayannan sirri fiye da dubu bakwai ga shafin kwarmata bayanai-Wikileaks, hukuncin daurin shekaru talatin da biyar a gida yari.

Mai shari'ar sojoji, ya kama Bradley Manning da laifin cin amana da kuma sata.

Manning wanda ya tsegunta bayannan sirri game da yakin Iraki, bai nuna nadama ba game da laifin da aka kamashi dasu.

Magoya bayansa sun jinjina masa a Maryland a lokacin da yake barin kotun.

Shafin Wikileaks ya bayyana hukuncin a matsayin nasara, saboda Manning zai soma walwala cikin shekaru tara.

Karin bayani