Mace ta so a kashe 'ya'yanta saboda inshora

Sojojin Afrika ta Kudu
Image caption Ana tuhumar matar da hada baki domin yin kisan kai kuma za ta gurfana a gaban kotu ranar Alhamis

'Yan sanda a Afrika ta Kudu sun ce sun kama wata mata, kuma sun tuhume ta da yunkurin kashe 'ya'yanta maza biyu saboda inshora.

'Yan sandan sun ce matar mai shekaru 50 dake garin Port Shepstone a kudu maso gabashin kasar, ta dauki hayar wani dan uwanta ya aika kisan gillar.

Sai dai mutumin ne ya fallasa shirinta ga 'yan sanda.

A sanarwar da 'yan sandan suka fitar, sun ce za a biya mutumin dala 2400, amma matar ta nemi a yi mata ragi saboda na gida ne.

Wacce ake zargin ta kuma yi wa mutumin alkawarin wasu ayyuka uku, idan har ya samu nasarar kashe 'ya'yan nata.