Luguden wuta a birnin Damascus

Image caption Ana zargin lamarin ya rusta da kananan yara

'Yan adawan Syria sun bada rahoton cewar dakarun gwamnati sun yita luguden wuta babu kakkautawa a yakunan dake wajen birnin Damascus.

A cewarsu, an kashe fiye da mutane dari daya sannan shaidu sun ce an yi amfani da sinadirai masu guba.

Gwamnatin Syria ta musanta rahotannin, amma hotunan bidiyo wadanda ba a tantance ba, sun nuna gawarwaki hadda na yara kwance suna kakari.

'Yan adawa na Syrian Observatory for Human Rights sun bukaci kwararrun kan sinadirai masu guba na majalisar dinkin duniya wadanda a yanzu haka suke cikin kasar, su ziyarci yankunan da abin ya shafa.

Editan Gabas ta tsakiya na BBC ya ce lokacin kai wannan harin ya dasa ayar tambayar game da abubuwan dake gunada a kasar ta Syria.

Karin bayani