An sanya takunkumi a kan 'yan Hezbolla

Shugaban kungiyar Hizbulla Hassan Nasrallah
Image caption Amurka ta sanya kungiyar hizbulla a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda a duniya

Amurka ta sanya takunkumi hana hada-hadar kudade a kan wasu mutane hudu.

Da ta ce manyan jami'an kungiyar gwagwarmayar islama ta Hizbolla da ke Labanon ne.

Ma'aikatar kudin Amurka ta ce mutanen hudu, Khalil Harb da Mohammed Kausarani da Mohammed Yusuf Ahmad Mansour da Mohammed Qabalan su na haifar da rashin zaman lafiya, da kuma tsara kai hare-haren ta'addanci a duk yankin gabas ta tsakiya.

Tun a shekarar 1997 Amurkan ta sanya Hizbolla a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya.

Karin bayani